Daga Aisha Aliyu Umar
Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya mai suna Hadiza Isma’il yar asalin karamar hukumar Madobi a kasar Saudiyya.
“Hadiza Isma’il daga karamar hukumar Madobi ta rasu a ranar Litinin da misalin karfe 3:15 na rana agogon kasar Saudiyya bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya”. A cewar sanarwar
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban tawagar yan jaridun kano a aikin Hajjn bana Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24 .

Sanarwar ta ce an kai matar mai shekaru 58 a asibitin NAHCON domin jinyar zazzabi kafin a kai ta asibitin Sarki Abdulaziz dake Makka inda aka tabbatar da rasuwarta.
Tuni dai aka binne ta a garin Makka bayan sallar jana’iza a masallacin Ka’aba.
Yadda Jam’iyyar APC ta Gabatar da Shaidu 5 Cikin 300 ga Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnan Kano
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ya mika ta’aziyyar hukumar ga iyalan mamaciyar a madadin gwamnan jihar Kano, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama ya kuma baiwa iyalai hakurin jure rashin.