Yadda Jam’iyyar APC ta Gabatar da Shaidu 5 Cikin 300 ga Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnan Kano

Date:

Daga Aisha Sani Bala

 

Jam’iyyar APC, ta gabatar da shaidu 5 daga cikin shaidu 300 da ta rubuta da farko don bayar da shaida a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito jam’iyyar APC, a matsayin mai shigar da kara, tana takara ne domin nuna kin Amincewa da ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a Kano.

Talla

Karar da jam’iyyar APC ta shigar ta fi karkata ne ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), a matsayin wadda ake kara ta daya da kuma Abba Kabir Yusuf, wanda ake kara na biyu, yayin da NNPP ta ke a matsayin wacce ake kara ta uku a shari’ar.

 

Idan za’a iya tunawa masu shigar da karar sun gabatar da shaida na farko wato PW1, inda babban lauyan jam’iyyar APC, Offiong Offiong SAN ya jagoranci gabatar da shi a gaban kotu.

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano ya nada masu bashi shawara na musamman 6, da MD Karota, Radio kano da sauransu

Justicewarch ta rawaito daga baya Lauyan hukumar INEC dana Abba Kabir Yusuf, da kuma Barr Oshayomi na jam’iyyar NNPP, Adegboyega Awomolo SAN, da AJ Owonikoko, SAN, suka yi wa shaidan tambayoyi.

 

A yayin da kotu ta sake zama a ranar Talata, domin ci gaba da sauraren karar, lauyan APC, ya gabatar wa kotun karin shaidu 4, inda suka bayar da shaidarsu.

Yadda Sanata Rufi’i Hanga da Aliyu Madakin gini suka sami mukamai a Majalisar kasa

A cikin shaidar da ya bayar, Ya’u Aminu, shaida na uku (PW 3), ya ce yana zaune ne a garin Shifawa dake karamar hukumar Gaya.

Ya ce ya bayar da shaidarsa a rubuce da harshen Hausa kuma lauyansa ya fassara ta zuwa Turanci.

Shaida na uku (PW 3), ya ci gaba da cewa shi wakilin APC ne a runfar zaben dake gidan yarin Shifawa, akwati Mai 006 a karamar hukumar Gaya.

A yayin tambayoyin da aka yi masa, shaidan ya shaida cewa ba ya iya rubutu da karatu shi ya sa ya bayar da shaidarsa da harshen Hausa.

Ya kuma shaida cewar babu wani tashin hankali da aka samu rumfa zaben da yayi aikin zaben.

Da yake cigaba da amsa tambayoyi, shaidan ya kara da cewa shi ba ma’aikacin INEC ba ne, wakili ne na jam’iyyar APC a lokacin zaben .

Ya kuma amince da cewa jam’iyyar sa ta mika dukkan sunayen wakilan ta ga hukumar zabe ta kasa INEC.

Shaidan ya musanta tambayar cewa ba a gano sunansa ba, a kundin sunayen wakilan APC da aka kai INEC a rumfar zaben Shifawa, akwai mai lamba OO1.

Tallah

Ya kara da cewa ba gaskiya ba ne da aka ce Isiyaku Alan shi ne Wakilin Jam’iyyar a rumfar zabe ta 001 ba shi ba.

Ya sake shaida cewa yana da takardar da aka bashi a matsayin wakilin APC da kuma katin shaida na INEC a zaben da ya gabata .

A yayin amsa tambayoyin, shaidan ya shaidawa kotun cewa ba a rubuta sunansa da sa hannun sa da kuma hoton babban yatsan sa a cikin takardar sakamakon zaɓen yankin ba.

Hakazalika shaida na ukun ya ci gaba da cewa ya yi rajista da jam’iyyarsa a matakin karamar hukumar, ba a matakin mazaba ba.

A cewarsa, a sanin sa an sami arin gizon kuri’u a akwatin sa da kuri’u 2.

Bayan bayar da shaidarsa, kotun mai alkalai guda 3 karkashin jagorancin Mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ta sallami Shaidan.

Hakazalika a cikin shedar da ya bayar, Kabir Muhd ​​shaida na hudu (PW 4) ya ce shi dan kasuwa ne kuma wakilin jam’iyyar APC a akwai mai lamba 005 dake mazabar Warawa.

A yayin da yake amsa tambayoyi da akai yi masa, shaida na hudu (PW 4) yace ba a sami tashin hankali a lokacin da ake zabe ba a akwatin rumfar zaben su.

Ya kara da cewacewa Amma an sami arin gizon kuri’u a rumfar zaben sa .

Shaidan ya kuma tabbatar da cewar jam’iyyar su ta tura sunayen mutune biyu da sunansa da na Haruna Dakata.

“Ina da takarda da jaket da INEC ta ba ni.” Yace.

A lokacin ne shaidan ya fito da takardar shaidar aikin da Rigar da INEC ta ba shi.

Ya tabbatar da cewa ba a rubuta sunansa, da dangwala babban dan yatsan sa ba a cikin takardar sakamakon .

Daga nan kotun ta sallami shaidan

Daga nan sai Aminu Baffa, Shaidan Jam’iyyar APC na biyar (PW5) daga mazabar Diso, rumfar zabe ta 007 a Makarantar Firamare ta Gwale, ya bayyana a gaban kotu, Inda ya bayar da shaidarsa, kuma aka yi masa tambayoyi.

Mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebe ya sallame, sannan ya dage zaman kotun zuwa ranar 5 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraron karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...