A wannan rana ta Laraba 05 ga watan Yuli gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yake jagorantar taron majalisar zartarwar jiha kano na farko tun bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.
Kadaura24 ta rawaito yanzu haka dai ana cigaba da gudanar da taron a karamin dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar kano, kuma Majiyar mu tabbatar mana cewa duk yan majalisar zartarwa sun halarci taron.