Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin masu bashi shawara na musamman da shugabannin wasu ma’aikatu a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Hisham Habib ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Wadanda aka nada a matsayin mashawarta na musamman ga gwamnan sun haɗar da :

1 Engineer Sulaiman Sani SA. irrigation and dams
2 Abdullahi Shuaibu SA Pension Fund Trustees
3 Yusuf Imam Shuaibu SA Youth and Sports
4 Sadiya Abdu Bichi SA Women Children and Disabled
5 Dr Nura Jafar Shanono SA Water Resources
6 Sanusi Sirajo Kwankwaso SA political Affairs
Yadda Sanata Ruf’iHanga da Aliyu Madakin gini suka sai mukamai a Majalisar kasa
Sannan sanarwar tace gwamnan ya kuma amince da nadi shugabannin wasu ma’aikatu a Kano
Wadanda aka nada din sun hadar da :
1. Engineer Faisal Mahmud Kumbotso MD KAROTA
2. Alhaji Abdullahi Rabiu MD Housing Corporation
3 Alhaji Ahmadu Haruna Danzago MD REMASAB
4 Hon Hisham Habib MD Radio Kano
Sanarwar tace nadin nasu ya fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.