Sarkin Kano ya dawo gida bayan kammala ibadar umarah

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Bayan kwashe kwanaki 8 yana gudanar da zirayar aikin ibadar Umrah Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya dawo Gida Kano.

 

Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin sauka a filin sauka da tashi na kasa da ksa na Aminu dake nan Kano tareda dan uwansa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Sarkin Bauchi Alhaji Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu.

Gwamna Ganduje ya nada Surajo Umar Wudil a matsayin SSA

Hakan na. Kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24.

A lokacin ziyarar aikin Umrah a kasa mai tsarki Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yana tareda Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

A lokacin saukar Mai Martaba Sarkin Kano ya sami tarba daga Hakimansa da sauran manyan yan Kasuwa tareda al’umar gari wadanda sukayi dafifi akan titi suna lale marhabun da zuwan uban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...