Ko ka san sau nawa zuciya ke harbawa kowace rana a jikinka ?

Date:

Daga Fatima Kabir Labaran

 

Masana sun tabbatar da cewa Zuciya ita ce famfon da ke harbawa domin buga jini zuwa dukan sassan jiki ba-dare-ba-rana domin ci gaban rayuwa. Rayuwa na tsayawa da tsayawar aikin zuciya.

 

Kwatankwacin girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum. Kuma zuciya tana bugawa sau 60 — 100 duk minti ɗaya yayin hutu, wato yayin da ba aiki ko motsa jiki ake yi ba. Saboda adadin harbawar zuciya [cikin minti ɗaya] na ƙaruwa yayin atisaye ko motsa jiki.

Ƙungiyar fitilar Jama’ar Bichi ta raba kayan Abinchi ga marayu da masu karamin karfi

A kowace rana kuwa, zuciya na harbawa kimanin sau dubu ɗari (100,000). Inda take buga jini da ya kai yawan galan dubu biyu a kowace rana. Har wa yau, zuciyar na buga jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 miles) in da za a warware tsayinsu.

 

Zuciya, sannu da aiki!

 

Daga shafin Physiotherapy Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...