Daga Nura Abubakar
Dan takarar majalisar wakilai na kura madobi da garun Malam Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya taya al’ummar Nigeria dana jihar kano musamman al’ummar Kura Madobi da Garun Mallam.
Musa Iliyasu kwankwanso ya bayyana hakan ne a wani sakon taya murnar cikar Nigeria shekaru 62 da samun yancin kai, wanda ya sanyawa hannu da kansa kuma ya aikowa Kadaura24.
Musa Iliyasu yace ya kamata yan Nigeria su cigaba da hadai kai da kaunar juna don tabbatar da dorewar kasar nan matsayin kasa daya al’umma daya, kamar yadda shugabannin farko irinsu Ahmadu Bello Sardauna da Tarawa Balewa sukai.
” Nigeria ta hadu da kalubale kala-kala tun daga lokacin da aka bamu yancin kai daga turawa mulkin mallaka, amma abun godiya ga Allah shi ne yadda har yanzu kasar na nan bata tana samun cigaba ta fannoni daban-daban”. Inji Musa Iliyasu
Yace a yanzu da ake da ake tunkarar babban zabe shekara ta 2023 akwai bukatar yan Nigeria su zabi yan takarar jam’iyyar APC domin sune zasu kai kasar nan ga tudun mun tsira.
” Muna fatan al’umma zasu dubi irin aiyukan alkhairi da jam’iyyar APC ta yiwa al’ummar Nigeria da kuma yadda gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta gudanar da aiyukan raya kasa da cigaban al’ummar jihar Kano”. Inji Kwankwanso
Dr. Musa Iliyasu kwankwaso ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano da kasa baki daya da su cigaba da yiwa shugabanni addu’a don su sami damar cigaba da yiwa al’umma aiki da kuma cigaba da hada kan kasar nan.