Kungiyar mu ta koyawa Mata da Marayu sana’o’in dogaro da kai – Baba Yawale

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Kungiyar tallafawa mata da marayu wato Orphans and women support initiative ta horar da mata da marayu 650 sana’o’i daban-daban domin su dogara da kawunansu .

Shugaban kungiyar Hon. Baba yawale ne ya bayyana hakan lokacin bikin yaye daliban wanda aka gudanar a dakin taron na State library dake jihar kano.
Baba yawale yace kungiyar ta fara gudanar da aiyukan tallafawa marayu da mata ne sakamakon mummunan yanayin da suke cintar kawunansu a cikin idan suka rasa masu kula da su.
Talla
” Babu shakka mun sami cigaba sosai idan aka kwatanta da shekarar data gabata, Inda muka yaye dalibai 350 amma a bana sun yaye dalibai 650 babu shakka dole mu godewa Allah”. Inji baba yawale 
Yace sun koyawa mata da marayun sana’o’i kala-kala sannan kuma suka nemar musu rancan kudin da zasu yi jari da su daga hukumar NISAL, Inda zasu biya bashi mara ruwan cikin shekaru uku, kuma sai sun yi shekara daya suna juya kudin kafin su fara biyan kudin.
” Wasu daga cikinsu zasu sami tallafin Naira Miliyan daya wasu dubu dari bakwai wasu kuma dubu dari uku duk dan sun rika gudanar da rayuwarsu cikin nutsuwa ba tare da sun rokin kowa komai ba”. A cewar shugaban kungiyar
Talla
A jawabinsa mataimakin gwamnan jihar kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Wanda Babban mataimaki na musamman akan harkokin kungiyoyi masu zaman Kansu a ofishin mataimakin gwamna Alhaji Abubakar Ya’u Indabawa ya yabawa kungiyar ta Orphans and women support initiative bisa gudanar da wannan gagarumin aikin.
Have kamata yayi kungiyoyi su yi koyi da irin wannan abun alkhairi da kungiyar ta gudanar Wanda zai iya zama sanadin shigar shugabanninta aljannah kuma sun tallafawa kokarin gwamnatin jihar kano na magance zaman banza a tsakanin matasa.
” Gwamnatin nan ta fito da hanyoyi daban-daban don koyar da matasa sana’o’in hannu don su dogara da kawunansu, saboda a yanzu gwamnati bazata iya baiwa kowanne matashi aikin gwamnati ba, don haka dole matasa su nemi sana’o’i don su dogara da kawunansu “. Inji Gawuna
Mataimakin gwamnan na kano ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su dage wajen yin amfani da abun da aka koya musu da kuma jarin da aka basu don su inganta rayuwarsu da ta yan uwansu baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanata Barau Jibrin ya zama Uban kungiyar tsofaffin yan majalisun Kano

Kungiyar tsofaffin yan majalisu ta kano sun nada mataimakin...

Babu wanda ya hana ni shiga Fadar Shugaban Kasa – Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa babu...

Komawar Kwankwaso APC: NNPP ta Kano ta fadi matsayarta

Daga Hafsat Lawan Sheka   Jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta...

Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria

Kamfanin albarkatun man fetur na Nigeria NNPCL ya rage...