Daga Hafsat Lawan Sheka
Jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a Kano.

Dungurawa ya ce Kwankwaso ba ya bukatar tuntubar kowa kafin ya yanke shawarar a siyasan ce, amma ya jaddada cewa ba su da wani shiri na sauya sheka zuwa APC.
“Ba mu da wata alaka da APC, kuma ba mu da niyyar komawa cikinta” in ji Dungurawa, inda ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa.
Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria
Ya bayyana wannan hasashe a matsayin maras tushe kuma ya ce makiya ne suke yada shi.
Ya kuma bayyana cewa suna da yakinin gwamnatin NNPP a jihar Kano na yin duk abubuwan da suka dace.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito makusanci Kwankwaso Buba Galadima ya fito ya musanta labarin cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC.
Kadaura24 ta ruwaito shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano na cewa kofar jam’iyyar a bude take ga Kwankwaso da sauran ‘yan Najeriya da ke son shiga cikinta.