Dawo da Gwadabe ya Jagoranci Anti Daba Hanya ce ta Magance Fadan Daba a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Rahotanni na tabbatar da cewa a kokarinta na magance fadan daga a jihar Kano Rundunar Yansandan jihar ta mayar da BM Gwadabe a matsayin O/C Anti daba .

Idan za a iya tunawa a Gwadabe ya taba zama O/C Anti daba gabanin yani dalili yasa a dauke shi daga wurin a karshen shekara ta 2023.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hakika a baya BM Gwadabe ya taka rawar gani wajen magance fadan daba a jihar Kano, sakamakon Salon da ya rika amfani da su wajen magance fadan, wanda hakan yasa da yawa daga cikin yan daban sun gudu wasu kuma suka hakura da harkar baki daya.

Sai dai bayan sauyawa Gwadabe wajen aiki fadan daba da kwacen wayoyi da babura ya dawo musamman a kananan hukumomin dake kwaryar birnin Kano, wanda hakan ya addabi mutane da yawa a jihar.

APC a Kano ta magantu kan yunkurin Kwankwaso na shiga jam’iyyar

A baya kadaura24 ta rawaito an kashe mutane da yawa sanadiyyar fadan daba da kuma wadanda aka kashe saboda ana son kwatar musu wayoyi ko kuma baburansu, lamarin da ya jefa al’ummar Kano cikin rashin kwanciyar hankali.

Gabanin azumi da cikin azumin da ya gabata fadan daba ya yi kamari sosai a unguwannin Dorayi, Kofar Mata, Yakasai, Zango da sauran manyan unguwannin a Kano.

Babu shakka kokarin da kwamishinan yansanda na jihar Kano ya yi na mayar da Gwadabe Anti daba ya nuna matukar kokarinsa na ganin an kawo karshen fadan daba a fadin jihar Kano.

InShot 20250309 102403344

Yanzu abun da ya kamata shi ne rundunar yansandan kano da shugabannin harkokin tsaro a Kano har ma da gwamnatin jihar Kano su baiwa BM Gwadabe cikakken hadin kai da goyon baya don cimma manufar mayar da shi.

Wani abun burgewa shi ne yadda al’umma jihar kano su ke murna da sake baiwa Gwadabe O/C na Anti daba, saboda suna da yakinin Gwadabe zai kawo karshe fadan daba a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...