Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa babu wanda ya hana shi shiga fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock Bill, inda ya bayyana labarin a matsayin mummunan rahotannin da ake yadawa.
A daren Juma’ar da ta gabata ne rahotanni a shafukan internet su ka bayyana cewa wasu jami’an tsaro sun hana mataimakin shugaban kasar shiga Villa, kuma an tsare shi a gidansa har sai shugaban kasa ya dawo daga tafiyarsa zuwa kasashen waje.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Mista Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, ofishin mataimakin shugaban kasar, ya ce labarin ba gaskiya ba ne.
Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria
A cewarsa, irin wadannan munanan bayanai ba za su iya nishadantar da su ba sai wadanda ba su san ayyukan cikin gida na gwamnatin Najeriya ba.
Ya ce, a ‘yan kwanakin nan, da gangan da kuma tsare-tsare aka yi ta shirya karya a kan ofishin mataimakin shugaban kasa ta fuskoki da dama.
Wannan yunƙuri ne na rashin na cin zarafin mutum da ofishin mai girma mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.
Nkwocha ya ce a farkon makon nan ne fadar shugaban kasa ta yi watsi da irin wannan labarin na karya dangane da alhakin yada hotunan yakin neman zaben da ke dauke da hotunan shugaba Bola Tinubu.
Ya ce Shettima ya ci gaba da mai da hankali kan ayyukan sa da kuma marawa shugaban kasa baya wajen cimma muradun ‘yan Najeriya.
Nkwocha ya yabawa ‘yan Najeriya a kowane bangare da ke ci gaba da nuna fatan alheri ga gwamnatin Tinubu kuma suka dauki nauyin yaki da yada labaran karya.”