Kamfanin albarkatun man fetur na Nigeria NNPCL ya rage farashin man fetur daga Naira 960 zuwa N945.

Kadaura24 ta tabbatar da hakan ne bayan da ta gudanar da bincike a wasu gidajen man NNPC dake birnin Kano.
APC a Kano ta magantu kan yunkurin Kwankwaso na shiga jam’iyyar
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito matatar mai ta Dangote a makon nan da muke bankwana da shi ta sanar da rage farashin man zuwa N835 mai makon yadda take sayarwa a baya.
Binciken Kadaura24 ya gano cewa Kamfanin NNPC din bai sanarwa al’umma raginba, amma ya rage farashin man akan kawunan da yake sayar da man a gidajen mai mallakin kamfanin.