Kungiyar tsofaffin yan majalisu ta kano sun nada mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin a matsayin Uban kungiyar .
A wata sanarwa da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a sashin shafinsa na Facebook ya ce kungiyar tsofaffin yan majalisun sun yi masa wannan nadin ne bisa la’akari da gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban majalisa a Nigeria.

” A safiyar yau ne ’yan kungiyar tsofaffin ‘yan majalisar dokokin Kano suka nada ni a matsayin Uban kungiyasu, bisa la’akari da irin kwazon da nake yi a majalisar da kuma gudunmawar da nake bayarwa wajen cigaban jihar Kano da kasa baki daya”.
Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria
kungiyar karkashin jagorancin shugabanta, Comrade Alhassan Uba Idris, da Sakatarensa Umar S Muhammad, sun ce sun nada Barau Jibrin ne bisa chanchanta da kwarewarsa wajen ta gudanar da aikin majalisa.
Sanata Barau Jibrin ya ce “Ina godiya ga shugabannin tsofaffin kungiyar ‘yan majalisa da suka ga na cancanci wannan nadi. Insha Allahu bazan ba ku kunya ba”.
Ya ce zai ci gaba da yin aiki tukuru domin ci gaban jihar Kano da kasa baki daya.