Daga Rukayya Abdullahi Maida
A karon farko tun cikin shekara ta 2015 mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya fita daga jerin mutum goma mafi arziki a Amurka.
Wani rahoton mujallar Forbes da ke tantance mutanen da suka fi kudi a duniya, ta ce Zuckerberg ya yi asarar fiye da rabin dukiyarsa – kimanin dala biliyan 76.8 tun cikin watan Satumban 2021, inda ya fadi daga mataki na uku a jerin mutum 400 mafi arziki a Amurka zuwa mataki na 11.

Da dukiyar da ta kai dala biliyan 57.7 a jerin masu kudin Amurka na bana, Zuckerberg na bin bayan Jim Walton da tsohon magajin birnin New York Michael Bloomberg.

Rahoton ya ce a duk fadin Amurka babu mutumin da ya kai Mark Zuckerberg tafka asara a shekarar da ta wuce. Forbes ta alakanta raguwar dukiyar tasa da faduwar darajar hannayen jarin kamfaninsa na Meta wanda ya ragu da kashi 57% tun bara.