Gorin rashin haihuwa yasa wata mata satar jariri a Bauchi

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

Jami’an tsaro sun kama wata mata da ake zargin ta saci jariri sabuwar haihuwa, Ibrahim Khalid a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

 

Jaridar Punch ta ce jaririn wanda ɗan tagwaye ne, an sace shi ne ranar Talatar makon jiya a dakin asibiti, kafin a gano tare da mayar da shi hannun mahafiyarsa.

Talla

Ana zargin wacce ta saci jaririn da yin shiga kamar ma’aikaciyar jinya a asibitin kuma ta lallaba ta zari yaron ba tare da an kama ta ba.

 

Bayanai sun ce wadda ake zargin ta sace jaririn ne saboda damuwar da ta shiga sakamakon yawan gorin da dangin miji ke yi mata na rashin haihuwa.

 

Talla

Wadda zargin ta kai jaririn kauyensu na Dull a cikin karamar hukumar Tafawa Balewa tana cewa dan da ta haifa ne.

 

Da a ke tuhumar ta, sai matar ta kada baki ta ce ta na shan horon rashin haihuwa ne shi ya sanya ta aikata wannan aika-aika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanata Barau Jibrin ya zama Uban kungiyar tsofaffin yan majalisun Kano

Kungiyar tsofaffin yan majalisu ta kano sun nada mataimakin...

Babu wanda ya hana ni shiga Fadar Shugaban Kasa – Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa babu...

Komawar Kwankwaso APC: NNPP ta Kano ta fadi matsayarta

Daga Hafsat Lawan Sheka   Jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta...

Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria

Kamfanin albarkatun man fetur na Nigeria NNPCL ya rage...