Bamu mu ka fitar da sunayen Yan kwamitin yakin neman zaben Tinubu ba – Lalong

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

Kwamitin yakin neman zaben Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, ya ce jerin sunayen da ake yadawa a shafukan sada zumunta da wallafa wasu a kafafen yada labarai na Internet cewa ba su da masaniya akan sunayen da ake yadawa.

 

Daraktan Yada Labaran kwamitin Mista Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, inda yace an wallafa wandannan sunayen ne ba da izinin kwamitin ba.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen, inda ya kara da cewa shugabancin jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu za su kaddamar da kwamitin yakin neman zaben nan gaba a hukumance.
Onanuga ya ce sun fahimci al’umma na kaunar jam’iyyar APC shi yasa ma suka kahu su San suwaye yan kwamitin yakin neman zaben dan takararsu na shugaban kasa.
Sai dai ya bukaci kafafen yada labarai da su yi taka tsantsan wajen yada labaran da ba su dace ba.
A lokacin da yake zantawa da sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mista James Faleke, Onanuga ya ce ana ci gaba da samar daraktoci daban-daban na tsarin yakin neman zaben.
Ya ce ana yin hakan ne tare da tuntubar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar don yin abun da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki

Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya...

Aiyuka 5 da Gwamnan Kano ya yi alkawarin yi, bayan dakatar da rusau a Rimin Zakara

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci garin Rimin Zakara...

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Daga Safiyanu Dantala Jobawa Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu...

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...