Gwamnatin jihar kano ta hana makarantar Kano Capital karin kudin makaranta ga dalibanta

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

 

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta umarci hukumar gudanarwa ta makarantar Kano Capital data janye sabon karin kudin makaranta data yi.

 

Babbar sakatariya a ma’aikatar Hajiya Lauratu Ado Diso ce ta bayar da wannan umarni yayin da take kaddamar da kwamitin da zai yi nazari kan rahotannin makarantar na baya da aka gabatarwa ma’aikatar domin aiwatarwa.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kai na ma’aikatar Ilimi Aliyu Yusuf ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 a ranar juma’a.

 

Babbar sakatariyar ta tabbatarwa iyayen Daliban da abun ya shafa cewar ma’aikatar zata tabbatar komin an dorashi kan gurbinsa, ta hanyar amfani da ka’idoji da kuma doka, inda ta bukace su dasu kwantar da hankalinsu sannan kuma su kasance masu bin doka.

 

Ta kara da cewa an kafa kwamitin ne domin yin nazari kan rahotanni baya na makarantar da aka gabatar masu game da wasu matsaloli da aka gano a makarantar domin aiwatarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...