Daga Abdulmajid Habib Isa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, yace yana da yakinin cewa jam’iyyar PDP za ta rushe da zar ya fita daga cikin jam’iyyar.
Kadaura24 ta rawaito Kwankwaso duk da cewa a halin yanzu baya jin dadin jam’iyyar,Amma ya bada tabbacin har yanzu yana Cikin jam’iyyar Bai Kai ga fita ba.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wani shirin gidan Talabijin na Channels, a cikin shirin Political Paradigm.
Kwankwaso ya yi tsokaci kan wasu dalilan da suka bayan jin dadin yadda ake tafi da jam’iyyar PDP, inda ya ba da misali da abun da faru a taron shiyyar Arewa maso Yamma da aka yi kwanan nan a Kaduna.
“Ya kamata in kasance daya daga cikin masu fada a ji a jam’iyya PDP,” Amma ana ganin ban Isa ba Kuma Wasu Suna raina matsayina a jam’iyyar wanda ni Kuma bazan lamunci irin wannan wulakancin ba.