Amurka ta ce ta yi gargaɗi ga China cewa babu wata ƙasa da za sha a koƙarinta na ceto ƙasar Rasha daga halin da ta shiga na takunkuman da aka ƙaƙaba mata kan hare-haren da ta ke kai wa a Ukraine.
Mai ba da shawara kan sha’anin tsaro na amurka Jake Sullivan ya ɗauko batun kai-tsaye inda ya bayyana damuwarsa a lokacin da yake tattaunawa da jami’in diflomasiyyar China Yang Jiechi, a birnin Rome na Italiya.
Ya ce Amurka tana kallon ta inda China za ta taimakawa Putin.
Kafin tattaunawar a Rome, Jami’an Amurka sun ce Rasha har ta nemi taimakon soji ga China. Gwamnatin China kuma ta bayyana ikirarin na Amurka a matsayin labarin kanzon kurege.