Daga Yakubu Masu Kano
Babban Darakta Janar na NYSC, Maj. Gen. Shuaibu Ibrahim, ya yabawa Majalisar wakilai ta kasa bisa ci gaban da aka samu a kan kudirin kafa Asusun Amintattu Shirin Masu yiwa Kasa hidima na NYSC.
Kadaura24 ta rawaito Shu’aibu Ibrahim ya yi yabon ne a ranar Talata a yayin faretin rufe sansanin Yan yiwa kasa hidima rukuni na farko na shekara ta 2022 a Kusalla dake karamar hukumar Karaye a jihar Kano.
“Ina son mika godiyata ga Majalisar Wakilai da kuma Majalisun kasa baki daya bisa ci gaban da aka samu kawo yanzu a kan kudirin kafa Asusun Amintattu, wanda aka yi masa karatu na Daya da na biyu kuma an gabatar da taron jin ra’ayoyin al’umma,” in ji shi.
Shu’aibu Ibrahim wanda Shugabar Shirin a jihar kano Hajjya A’isha tata Muhammad ta wakilce ta, ya bukaci ‘yan yiwa kasa hidimar da su yi Aikin da Sana’o’in da suka koya a yayin zamansu a sansanin don su dogara da kawunsu .
Ya kuma shawarce su da su karbi rigakafin COVID-19 musamman ga Waɗanda ba a riga an yi su ba, sannan ya umarce su da su taimaka wajen wayar da kan al’ummomin da aka turasu cikin su muhimmancin allurar rigakafin da kuma bin matakan kariya daga Corona.
Darakta Janar din ya bayyana jin dadinsa ga Gwamnatin Tarayya bisa bayar da damar Sanya yan yiwa kasa hidimar a tsarin Inshorar Lafiya ta Kasa a karkashin wani gagarumin shiri da aka fi sani da NYSC Group Individual Family Social Health Insurance Program (GIFSHIP).
DG Shu’aibu Ibrahim ya yi kira ga daukacin Masu yiwa kasa hidimar da su ci gajiyar wannan tsari ta hanyar yin rijista a karkashin a wuraren da aka turasu, kuma a ko da yaushe su ruki Zuwa Asibitin Masu kusa da su Idan sun ji alamu na Rashin Lafiya domin su sami kulawar likitoci.
Ya yi kira ga Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnati da Masu zaman kansu da su karbi Masu yiwa Kasa hidimar da aka tura musu su kuma basu kulawar da ta dace.
Ibrahim ya bukaci ’yan yiwa kasa hidimar da su kasance masu lura da tsaro a kowani lokaci tare da mutunta al’adu da dabi’u tare da bayar da kyakykyawar gudumawar ci gaban al’ummar da suke zaune.