Bazan Sake Fitowa a Cikin Shirin Labarina ba – Nafisa Abdullahi

Date:

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Labarina’ ba.

Kadaura24 ta rawaito a sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta.

A Sanarwar da ta Fitar Nafisa tace harkokin Kasuwancinta da Makaranta ne Suka hana ta cigaba da fitowa a Shirin,Inda tace Suna da kyakykyawan fahimta da Kamfanin Saira movies Kuma ba Wata Matsala Suka samu ba.

Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.

Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...

NUJ@70: Gwamnan Kano ya karbi lambar girmamawa daga yan jarida

Daga Rukayya Abdullahi Maida Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nigeria (NUJ)...