Daga Rukayya Abdullahi Maida
Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nigeria (NUJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta musamman bisa goyon bayan da yake bai wa aikin jarida.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Muhammad Idris, ne ya miƙa lambar girmamawar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu
An bayar da lambar karramawar ne yayin bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafuwarta a birnin Abuja, inda mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karɓa a madadin gwamnan.
Shugaban NUJ na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ya ce an zaɓi Gwamna Abba ne saboda irin goyon bayan da yake bai wa kafafen yaɗa labarai da kuma jajircewarsa wajen cigaban ƙasa, kare ’yancin fadar albarkacin baki da inganta shugabanci na gari.

A nasa jawabin, mataimakin gwamnan ya taya Gwamna Abba murna, yana mai cewa karramawar ta nuna yadda gwamnatin Kano ke mutunta aikin jarida da ma dimokuraɗiyya baki ɗaya.
Kwamared Gwarzo ya kuma bayyana cewa Jihar Kano za ta karɓi bakuncin taron Kungiyar NUJ na gaba.