Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Date:

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da laifin gurɓata muhalli da karan da kekensa ke yi.

Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar ce ta kai ƙarar telan mai suna Mubarak Yusuf, kan yadda keken ɗinkinsa da kuma injin janareto ke damun mutanen anguwa da daddare.

InShot 20250309 102512486
Talla

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce duk da cewa ya musanta zargin, amma ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da kotun.

Har ila yau, kotun ta kai ziyarar gani da ido shagon da telan ya ke aiki, inda kuma ta tabbatar da cewa karan kekensa yana hana mutane barci da daddare, abin da ya saɓa wa sashi na 7 na dokar kare lafiyar al’umma ta 2019.

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

“Don haka ne kotun ta yanke hukuncin taƙaita masa lokutan yin aiki, inda yanzu zai riƙa aiki daga karfe 6:00 na safe zuwa 9:00 na dare,” in ji sanarwar.

Kwamishinan muhalli na jihar ta Kano, Dakta Dahir Hashim ya yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya ƙara nanata zimmar ma’aikatar na ganin ta tabbatar da cewa kowane mutum ko kuma wuraren kasuwanci sun bi matakan kare lafiyar al’ummar da kuma muhalli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...