Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Babban Darkatan Hukumar Samar da gidaje ta Kasa Kuma tsoho Dan Majalisar wakilai Wanda ya wakilci Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji Hon Abdulmumini Jibril Kofa ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Lagos Asiwaji Bola Ahmad Tinubu ya na da cikakkiyar Lafiyar da Zai iya Shugabantar Nigeria a Shekara ta 2023.
Abdulmumini Jibril Kofa ya bayyana hakan ne yayin Wani taron bada tallafi ga matasa 2500 da yiwa kasa addu’a Wanda aka gudanar a Gidansa dake Garin Kofa a Karamar Hukumar Bebeji.
Kofa yace batun Rashin lafiya Kowa Yana yi, Amma yace Yana mamakin yadda aka damu da batun Lafiyar Tinubun Wanda Kawai Rashin lafiya yayi kamar kowa Kuma ya warke.
Yace kamata yayi Mutane Sufi Mai da hankali Kan chanchanta da kwarewar da Tinubu ke da ita ta fuskar tattalin arzikin da Kuma kokarin da yayi na dora Jihar Lagos a Kan tafarkin cigaba.
Kofan Wanda shi ne Babban Daraktan Kwamitin koli na yada an gizon Bola Tinubun ya bada tabbacin Bolan Zai fito takarar Shugabancin Kasar nan a Shekara ta 2023.
Dangane da batun Sulhun da ake kokarin yi tsakanin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Gwamnan Rabi’u Musa Kwankwaso Kofa yace Yana goyon bayan Sulhun wanda yace idan aka yi shi Zai taimaka wajen cigaban Jihar Kano.
Da yake Mika tallafin kudade ga Matasa maza da Matan da Suka Amfana Abdulmumini Kofa yace ya bayar da tallafin ne domin tallafawa yunkurin Gwamnati na kawar da talauci da Zaman banza tare da inganta Ilimi Mata a Yankin.
Yayin taron an baiwa mata tallafin kudin makaranta ,su Kuma Matasa maza aka basu tallafin yin sana’o’i don inganta Rayuwar su, Waɗanda Suka Amfana da tallafin sun fito ne daga yanki Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji.