‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan ya bude ayyuka 7 cikin 556 na Gwamna Zulum

Date:

Daga Rabi’u Yusuf Madatai

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gagara boye farin cikinsa a yau Alhamis a Maiduguri bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin 556 da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya aiwatar cikin shekara biyu da ya yi a kan karaga.

“Ina jin matukar gamsuwa da salon mulkin Mai Girma Gwamna Babagana UMara Zulum yake gudanarwa a Jihar Borno cikin shekara biyun da suka gabata”. Inji Buhari

‘’Mutum ne ba mai nuna son kansa ba sannan yakan sa kansa cikin hadari domin kawai ya tabbatar da al’ummarsa ta zauna lafiya cikin jin dadi.

‘’Na so a ce duk wani wanda ke jagorantar al’umma a kowane mataki ya yi koyi da Gwamna Zulum maimakon ya tsaya yana ta kame-kame tare da daukar laifinsa ya maka wa wani.

Buhari ya kara da cewa ce zaga inda na bude wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Zulum ta gudanar cikin shekara biyu tana mulki.

Shugaban ya yi magana kan aiki guda daya tak na Cibiyar Koyar da Sana’o’i wacce ya bude a Muna, inda ya bayyana shi a zaman ‘’Sara a kan gaba da ya zo dai-dai da bukatar da ake da ita ta koyar da sana’o’i tare da samar da ayyuka’ wanda zai taimaka wajen rage dimbin matasan da ba su da abin yi a jihar da hakan zai hana su shiga ayyukan ta’addanci.

An tsara cibiyar domin koyar da matasa 1,500 a shekara tana da bangaren koyar da sana’ar kanikancin mota da gyaran laturoni da hada wutar sola sarrafa fata da kirgi sana’ar aski da kwalliya da gyaran waya da walda aikin gini da kafinta da harkar fasahar sadarwar zamani da dinki da dai sauran sana’o’i.

Sannan a cibiyar akwai dakunan kwanan dalibai har kimanin 200 da kicin da dakin shakatawa da ofishin gudanarwa da ma wuraren wasanni.

Sauran ayyukan da Shugaba Buhari ya bude sun hada da Jami’ar Jihar Borno wanda gwamnatin Zulum din ta gina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...