2023: Khalifa Muhd Sanusi II ya Magantu Kan Kiraye-Kirayen yin takara

Date:

Daga Khamis Musa Sidi


Sarkin Kano na 14 Kuma Shugaban Darikar Tijjaniyah na Nigeria Khalifa Muhammadu Sanusi na II ya bayyana matsayarsa Kan kiraye-kirayen da ake yi Masa na ya fito neman takara a kakar Zabe Mai zuwa ta 2023.


Khalifa Sanusi yace bashi da niyar Neman Wata kujerar Siyasa a Kasar nan,Inda yace kujerar da yake Kai ta khalifanci Tijjaniyah shi a wajensa tafi ta Shugaban Kasar Nigeria.


Khalifa Sanusi ya bayyana hakan ne Yayin daya jagoranci Mukaddamai da mabiya Tijjaniyah na Kasa a Abuja.


” Ni ban taba sha’awar shiga harkokin Siyasa a Nigeria ba ,Kuma ni a ganina ban ce a ganin Wasu ba a ganina kujerar khalifanci Shehu Ibrahim Inyass tafi kujerar Shugaban Kasa” inji Khalifa Muhd Sanusi II

Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ce ba shi da ra’ayin neman wani mukamin siyasa a Najeriya, sai dai ya ce zai ci gaba da fadakar da al’umma a kan irin shugabannin da suka cancanta su zaba.

Khalifan ya bayyana cewa Rashin Ilimi shi ne babbar Matsalar Kasar mu Nigeria ,Inda yace ya Zama wajibi kowa ya bada tashi Gudunmawar domin dai-daita al’amuran a Kasar Nan.


Ya Kuma yi Kira ga Yan Nigeria dasu zauna Lafiya da juna don cigaban Kasar

117 COMMENTS

  1. Джошуа назвав головну загрозу з боку Усика в майбутньому Усик Джошуа смотреть онлайн Sky Sports Він переконаний, що Олександр Усик розпочне бій активніше, а чемпіон буде спершу вичікувати. Але Вайт наполягає, що у проміжку між 5-м та 7-м раундами Джошуа переможе Усика нокаутом.

  2. Усик – Джошуа: появились промо Энтони Джошуа Александр Усик 2021.25.09 Українець Олександр Усик (18-0, 13 КО) зможе нокаутувати британського чемпіона Ентоні Джошуа (24-1,22 КО). При цьому для нашого співвітчизника не стане проблемою перевагу суперника в габаритах

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...