Rahotanni daga Karama hukumar Rano dake jihar Kano a Nigeria na tabbatar da cewa a yau ne wani rikici ya ɓarke a karamar hukumar biyo bayan zargin mutuwar wani matashi mai suna Abdullahi Musa a hannun ‘yan sanda yayin da ake tuhumarsa.
An dai tuhumi matashi ne da laifin saɓa dokar hanya, lamarin da ya janyo ƴansanda su ka tsare shi, wanda hakan ya janyo zanga zanga a garin.

Yanzu haka dai zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a lokacin da masu zanga-zangar suka cinna wa ofishin ‘yan sanda wuta.
Gwamnatin Kano ta kama na’urorin da ake buga hotunan batsa
Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya ta’azzara ne bayan da aka ce ‘yan sanda sun bude wuta kan masu zanga-zangar, inda wasu matasa biyu suka jikkata.
Hakan tasa matasan garin suka kone ofishin yansandan tare da jikkata DPO.
Kadaura24 ta rawaito da yake tsokaci kan faruwar lamarin, Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za su gudanar da bincike tare da daukar matakan da suka dace.