Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jami’an ƙungiyar agaji ta Red Crescent sun karɓi haihuwar wata mata da naƙuda ta tasar mata a Masallacin Manzon Allah (S A W) da ke Madina.
Shafin da ke kula da masallatai biyu masu daraja na Saudiyya Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook a yau Juma’a.

Jami’an Red Crescent din sun je ne bayan kiran gaggawa da aka yi musu.
Bamu janye tuhumar da muke yiwa Tukur Manu ba – DSS
Bayan nan ne kuma sai aka kai mai jegon da jaririnta wani asibiti Jibril Health Center don ci gaba da kula da su.
Mahaifin jaririyar tuni ya raɗa mata suna Taiba, kamar yadda shafin ya ruwaito.