Bichi da makwabtan ta zasu yi adabo da matsalar wutar lantarki – Engr. Abba Bichi

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

 

A jiya alhamis ne zababben dan majalisar Tarayya Mai Wakiltar Bichi, kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayya Engr. Abubakar Kabir Abubakar ya jagoranci ma’aikatan Hukumar TCN da KEDCO domin kunna wutar Lantarki a sabon gidan wuta daya kawo Kuma yadaukin nauyin duk aikace-aikacen da akayi da kuma Katangeshi a karamar hukumar Bichi.

 

“Gidan wutar zai dauki kananan Hukumomi 14 dake kewaye da Bichi awa 24 idan ta dauke toh sede matsala ce daga National grid”. Inji Abba bichi

 

Yayin da yake jawabi a wajen taron kunna wutar Engr. Abubukar Bichi yace an samar da aikin wutar lantarkin ne domin inganta rayuwar al’ummar bichi da kewaye da kuma kara bunkasa tattalin arzikin yankin.

 

Talla

Ya ce idan wutar lantarki ta fara aiki gadan-gadan al’ummar yankin zasu yi adabo da matsalolin hasken wutar lantarki, kuma zai samar da aiyukan yi ga matasa masu yawa sosai.

 

Hukumar TCN ta yabawa Dan Majalisar bisa yadda ya fitar dasu kunya ya dauki nauyin aikin da za’ayi shekaru dayawa anayi amma yayi musu a Kasa da shekara 2 a don haka suka ce a sanyawa gidan wuta suna Abubakar Kabir Abubakar Sub-Station Bichi.

Sabuwar tashar wutar lantarki dake Bichi

Za dai ayi babban bikin bude wannan gidan wuta a wata ne watan December, inda ake sa ran Ministan Wutar lantarki da MD na TCN da Gwamnan Jihar Kano da Mai Martaba Sarkin Bichi zasu Jagoranci budewa katafaren tashar wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...