Bamu janye tuhumar da muke yiwa Tukur Manu ba – DSS

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

 

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta kasa wato DSS, ta ƙaryata batun cewa ta janye ƙarar da take yi wa fitaccen mai shiga tsakani da masu tayar da ƙayar bayan nan, Tukur Mama.

 

A jiya Alhamis ne wasu kakafen yaɗa labarai suka ce DSS ta janye ƙarar da ta shigar ɗin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na neman ta ci gaba da tsare shi tsawon kwana 60.

 

Jaridar Daily Trust ta ce labarin da aka fara yaɗawan ya ce lauyan DSS A. M. Danlami, ya shaida wa Mai Shari’a Nkeonye Maha jim kaɗan cewa an janye ƙarar saboda wasu abubuwa da suka taso.

Talla

Amma a wata hira da Daily Trust ta yi da mai magana da yawun DSS Peter Afunanya, ya bayyana labarin a matsayin ƙarya ne.

 

Afunanya ya jaddada cewa hukumar DSS ba ta taɓa janye ƙarar Mamu da ta shigar ba, yana mai cewa ana ci gaba da shari’ar.

 

Tun a watan Satumba ne DSS ta kama Tukur Mamu, wanda ya suna sosai wajen shiga tsakanin masu satar mutane da dangin waɗanda aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...