Daga Ibrahim Abubakar Diso
Usman Bin Zubair ya lashe zaben fidda gwani na Dan Majalisar dokokin Jihar kano cikin jam’iyyar APC daga Karamar Hukumar Gwale.
Baturen zaben fitar da gwani na majalisar dokoki ta jihar kano a karkashin jam’iyyar APC a karamar hukumar Gwale Alhaji Danlami Zakari unguwar gyattai ya sanar da cewa Usman Bin Zubair ya lashe zaben kuri’u Masu yawa.
Alh Danlami Zakari ya bayyana hakan ne jim kadan da kammala jefa kuru ‘u da dalagate sukai a ofishin hisba dake Gwale, yace Usman Bin Zubair ya sami kuru’u arbain da shida 46 cikin hamsin da aka jefa .
An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali , sannan Alh. Danlami Zakari ya yabawa mahukuntan jam’iyya APC da Jami’an tsaro bisa gudunmawar da suka bayar har zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.