Daga Safyanu Dantala Jobawa
Tsohon kwamishinan raya karkara na jihar kano Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya lashen zaben fidda gwani na takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura/Madobi/Garun mallam.
Yayin zaben Musa Kwankwaso ya lashe zaben ne da kuru’u 150, yayin Dan Majalisa Mai Wakiltar yankin Hon Kabiru Danhassan ya sami kuru’u 4, sai kuma Hajiya Hama Ali Aware Garun mallam ta sami 6.
Musa Iliyasu Kwankwaso dai tsohon Kwamishinan Ma’aikatar raya karkara ne a zamanin mulkin Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Yanzu dai Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso shi ne zai wakilci jam’iyyar APC a Babban zabe Mai zuwa na shekarar 2023, Inda ake ganin Zai iya yin nasara Saboda farin jinin da yake da shi a wurin al’ummar yankin Kura Madobi da Garum mallam.