Kotu ta wanke matar Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da kisan Hanifa

Date:

Wata kotu a nan Kano ta sallami Jamila Muhammad Sani matar Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da kashe ɗalibarsa Hanifah Abubakar.

Kotun Majistare mai Lanba 12 ƙarƙashin mai shari’a Muhammad Jibril ta wanke Jamila a zaman kotun na ranar Juma’a kan zargin da ake mata na ɓoye Hanifa.

Tun da fari dai Lauyan gwamnati Barista Lamiɗo Soran ɗinki ne Lauya mai gabatar da ƙara, kuma kotun ta yi la’akari da bayanan da Jamila ta bayar tare da yin nazari inda ta gano bata da wani laifi a kan batun sace Hanifa Abubakar da kuma kasheta.

Rahotannin sun rawaito Jamila tana cike da farin ciki sakamakon wanke ta da kotun ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...