Dole ne yan Nigeria su dage da yawaita addu’o’i a kwanaki 10 Zulhijja – Sheikh Muhd Nasir

Date:

Daga Usman Hamza

Shugaban majalisar limaman masallatan juma’a na Nigeria sheikh Muhammad Nasir Adam ya bukaci Al’ummar kasar nan da su dage wajan nema gafara da kuma yawaita aiki nagari a cikin kwanaki goma na farkon watan Zulhija da mu ke ciki.

Sheikh Nasir Adam ya yi wannan jawabin a kasa mai tsarki ta cikin wani sako da ya aikowa Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sheikh Nasir ya ce Wadanan kwanaki ne da bawa zai kara zage dantse wajan ibada, kamar yin sallar farillah cikin Jam’i, biyemasu da nafil-file, zakiri da salatin Annabi S A W harama da yin ibadar Azumi inda Allah yaba mutun iko.

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da kashe sama da Naira Biliyan 51 don gudanar da wasu aiyuka

kazalika Sheikh Muhammad Nasir Adam yace duk Wani mumini a irin wannan lokaci yana kokarin aikin da Allah zai kara yadda da shine domin kara kusanci ga mahalicci.

Da yake bayani ga maniyatan Nigeria wadanda su ka amsa kiran Allah ya bayyana cewa lailai ne su matsa da addu’a ga kawunansu da kuma kasa Nigeria da jihohinsu domin samun zaman lafiya da yalwar arziki.

InShot 20250309 102403344

Daga karshe shugaban majalisar limamin masallatan juma’a na Tarayyar Nigeria sheikh Muhammad Nasir Adam yayi addu’a ga Malamai ,’Yan Kasuwa, Ma’aikata, dalibai, matasa, Shugabani da sauran Al’ummar Gari akan neman taimakon Allah a cikin lamarinsu.​

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...