Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta zabi shugaban gidan Radio Freedom Ado Sa’idu Waraka a matsayin shugabanta.
Hakan na kushe ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Aminu Nuraddeen Aminu ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta ce anyi zaben shugabannin kungiyar ne a wani babban taro da ta gudanar a yau Asabar a Cibiyar yan Jarida ta Kano.
Wadanda aka zaba sun hada da shugaba Ado Sa’idu Warawa, Aishatu Sule mataimakiyar shugaba.
Aminu Nuruddeen Amin Secretary, Sani Yusuf Hanga Treasurer da Muhammad Aminu Jolly Sakataren Yada Labarai.
Da yake jawabin mika mulki shugaban kungiyar mai barin gado Prince Daniel Aboki, ya bukaci sabbin Shugabannin da su Maida hankali wajen ciyar da kungiyar gaba.
A jawabinsa na karbar ragamar shugabancin kungiyar sabon shugaban Ado Sa’idu warawa a madadin sauran wadanda aka zaba, ya ce sabon shugabancin zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa harkokin yada labarai sun inganta ana yin su bisa Kwarewa da bin ka’idojin aikin.
Sabon shugaban ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai da su ba da goyon baya don cimma manufofin da aka sanya a gaba.