Bayan jingine batun janye tallafin mai, an daina wahalar mai a kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gidajen Mai Musamman a Jihar Kano sun dawo aiki ka’in da na’in,tun bayan da gwamnatin tarayya ta bayyana Cewa ta janye Kudirinta na janye tallafin man fetur a Kasar nan.

KADAURA24 ta rawaito a baya dai al’umma da dama sun yi ta kokawa Kan yadda aka Rika Samun layi a Gidajen Man tare Kuma da tarar da Wasu gidajen a kulle, baya ga rufe gidajen man da suke yi ba lokutan da Suka Saba ba.
Hakan ta jifa al’umma da yawa Cikin firgici da damuwa Saboda yadda ake bata lokaci kafin a Sha man, Wasu lokutan akan bata aƙalla sama da mintina 30 zuwa akwa daya gabanin mutum yasha man a nan kano.
A mafi yawan lokuta al’umma Suna zargin cewa ana sane aka kirkiri wahalar man fetur din saboda a azaftar da al’umma da kuma tunani boye man don indan anyi Karin suci kazamar riba.
Amma Kuma tun lokacin da gwamnatin tarayya a fito karara ta bayyana cewa ta jingine Kudirinta na janye tallafin man fetur din, sai al’amuran bada man fetur din a gidajen man fetur dake jiha kano Suka sauya aka daina ganin layin, Kuma duk an bude kawunan ana bada man tare Kuma da Kaiwa har dare ana bada man fetur din.
Wasu Mutane a birnin Kano da Jaridar Kadaura24 ta zanta da su akan wannna lamari sun ce dama ana sane aka kirkiri wahalar man fetur din, Kuma sun yabawa Gwamnatin Buhari bisa jingine Kudirinta na janye tallafin man fetur din.
“Ya kamata masu gidajen man fetur su Rika tausayawa al’umma su taimaka wajen bada Gudunmawa don talaka ya Sami saukin rayuwa ,ba wai su jefa talakawan cikin halin kakanikayi ba”. Inji Wasu Mutane a Kano.
Yanzu dai a Kano an daina wahalar man fetur Sakamakon yadda masu gidajen man suke bada shi a koda yaushe Kuma mafin Yanzu suna sayar da man har da daddare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...