Daga Kabiru Muhd Getso
Kungiyar Ma’aikatan Ofishin Shugaban majalisar wakilai Femi Gberjabiamila (Gbaja Professinals Volunteers Network ) da hadin kwiwar Kungiyar Malaman gaba da sakandire ta yankin Dawakin Tofa sun Dauki Nation Karatun daliban yankin har su 130 tun daga matakin firamare.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban ma’aikatan ofishin Shugaban majalisar Hon Sunusi Garba Rikiji wanda ya wakilci Shugaban majalisar ya bayyana cewar wannan tsari somin ta6i ne, domin zasu cigaba da aiwatar dashi a sassa daban-daban dake fadin kasarnan.
Ya kara da cewar Shugaban majalisar kullun zuciyarsa a bayyana take wajen daukar Nigeria a Matsayin dunkulalliyar kasa baki daya, shi yasa kullum yake kokarin aiwatar da shirin tallafawa karatun kananan yara a kowanne yanki a kasar nan.
Daga Cikin Albashin Sa, Shugaban Kano Poly ya sake Rabon Naira Dubu Biyar-Biyar a Dawakin Tofa
Shi ma a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Hon Ado Tambai Gwa wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Garba Yusif Labour ya nuna farin cikinsa bisa wannan kabakin arziki da karamar hukumar Dawakin Tofa ta samu, inda ya bayyana gamsuwarsu da irin wannan gudummuwa da suka samu, ya Kuma ja hankalin Sauran al’umma masu rike da madafun iko da suyi koyi da wannan kyakkyawan tsari.
A karshe Hakimin Dawakin Tofa Alh Isma’il Umar Ganduje ya bayyana jin dadinsa bisa wannan abin alheri tare da fatan A’ummar da suka taru a wajen kaddamarwa sun koma gida lafiya.