Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar Kula da kafafen Labaran Radio da Talabijin ta Ƙasa (NBC) da ta faɗaɗa aikinta zuwa ga kafofin yada labarai na intanet, domin dakile yada bayanan karya da ke tayar da rigima a kafafen sada zumunta na zamani.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a taron Africast 2025 da hukumar NBC ta shirya a birnin Legas, inda kwararru da masana suka tattauna kan ci gaban harkar watsa labarai a ƙasar.

A cewar sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya aikowa Kadaura24, Gwamna Yusuf ya nuna damuwa kan yadda wasu tashoshin intanet ke yada labarai masu rarraba kan jama’a, musamman kan addini da siyasa.

Ya ce irin wannan abu na iya zama barazana ga zaman lafiya da haɗin kai a Nigeria.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin labarai ya yaba da wannan kira, yana mai cewa majalisar ta riga ta fara aikin gyaran dokar NBC domin ta ba hukumar ikon kula da kafafen watsa labarai na intanet yadda ya kamata.

Wannan kira na Gwamna Yusuf ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa na inganta aikin jarida, ƙarfafa ilimin amfani da kafafen zamani, da kare maslahar jama’a a duniyar sadarwar zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...