2023: Bayan Rikicin APC a Gombe, Jam’iyyar ta Sulhunta Danjuma Goje da Gwamna Yahaya Inuwa

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam

 

Kwamitin Rikon Jam’iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya sulhunta tsakanin Gwamna Muhammad Yahaya Inuwa na Jihar Gombe da kuma abokin burmin sa na siyasa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Ɗanjuma Goje.

Jami’in Yaɗa Labarai na Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar, Mamman Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar data gabata a Abuja.

Sanarwar ta ce Buni, da Shugaban Kwamitin Sulhu na APC, Sanata Abdullahi Adamu da tsohon Gwamnan Jihar Borno Kashim Shattima, mamba a kwamitin, su ne su ka jagoranci sulhun.

Sanarwar ta ce wannan shi ne karon farko da manyan ƴan siyasar na Gombe su ka haɗu tun bayan da rigimar siyasa ta ɓarke tsakanin su a shekarar bara.

Mai Mala Buni, Matsayin sa na Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar APC ta kasa ya baiyana jin daɗin sa game da sulhun da a ka yi.

Ya kuma yi alwashin sulhunta duk masu ruwa da tsaki a APC domin ƙarfafa jam’iyar yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...