Daga Yanza Dole ne Gwajin Corona Ga Masu Ziyartar Fadar Shugaban Kasa – Garba Shehu

Date:

Daga Aisha Abubakar Mai Agogo
Fadar shugaban kasa ta ce za a rika yiwa duk Wani bako da zai shiga fadar shugaban kasa da ke Abuja gwajin Covid-19 kafin a ba shi izinin shiga.
Kadaura24 ta rawaito Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
 Yace an tanadi kayan gwaje-gwajen COVID-19 cikin sauri Waɗanda zasu bayyana Sakamakon cikin ‘yan mintuna kaɗan a gani ko Mutum yana dauke da cutar ko bashi da ita.
 A cewar mai magana da yawun Shugaban Kasar, sabuwar dokar ta zama dole saboda karuwar adadin masu cutar COVID-19 musamman nau’in Omicron a duniya.
 Daily News 24b ta rawaito Shehu ya ce duk wani bako, in ban da wasu shugabanni, sai an yi masa gwajin Covid-19 a Kofa kafin a barshi ya shiga Villa.
 “Eh, an sanya sabon tsarin dokar gwajin COVID-19 ne ga duk masu ziyara a Villa,amm ba don gwamnoni kadai ba,” in ji Shehu.
 “Kowane mai ziyara a Villa, ba kawai wadanda ke ganin shugaban kasa ba, yanzu ana bukatar yin gwajin gaggawa a kofar gidan kafin a shiga don gudun yada cutar a Gidan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...