Daga Zara Jamil Isa
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar NRC, Alhaji Bashir Tofa ya rasu.
Wata majiya da ga iyalan mamacin ta ce ya rasu ne da asubar yau Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.
Kadaura24 ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne dai a ka fara raɗe-raɗin cewa Tofa ya rasu, in da dangin sa su ka tabbatar da cewa bai rasu ba, amma bashi da lafiya.
Allah ya jiqanshi Allah yayi masa rahma, Allah y kyauta namu xuwan