Daga Zara Jamil Isa
Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Kano Dr Ali Haruna Makoda ya bayyawa duniya cewa shi har Yanzu bashi da burin tsayawa takarar Kujerar Gwamnan Kano ko ma Wata Kujerar mulki.
KADAURA24 ta rawaito Dr. Ali Haruna Makoda ya bayyana hakan ne yayin da ya yake gabatar da Jawabi a wajen taron Kungiyar tsofaffin Daliban Makaranatar Sakandire ta kafin Hausa yan aji na Shekara ta 1988.
” Ali baya neman wata Kujerar mulki a Shekarar ta 2023 sai Kujerar da Allah ya zaba Masa wadda zata Zama alkhairi a gare ni da ku da duk al’ummar Jihar Kano baki daya,tun da zabin Allah shi ne dai-dai”. Dr Ali Makoda
Dr. Makoda ya roki ‘ya’yan Kungiyar da su taya su da yin addu’o’in kammala aikin da aka dora musu lami Lafiya Kamar yadda Suka Fara Lafiya.
An dade dai ana kiraye-kirayen Shugaban Ma’aikatan ya fito neman kurejar Gwamnan jihar Kano Saboda irin Gudunmawar da ake ganin zai iya bayar wajen cigaban Jihar nan idan ya Sami dama.