Daga Usman Usman
Ambassador Maryam Hassan shugabar kungiyar wayar da kan Al’umma da taimakawa wadanda suka fada shaye-shaye ta League for Societal Protection Against Drugs Abuse (LESPADA) ta ce matukar al’umma ba su tashi tsaye waje yaki dakile shada da fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ba, zai yi wuyar a magance barazanan tsaro, talauc da jahilci .
Amb. Maryam Hassan ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wakilin Kadaura24.

Ya ce suna kokari wajen bada ta wu gudunmawa a cikin wannan al’umma don Samun matasa masu kishin cigaban kasa Samar da aikinyi domin inganta Rayuwa jama’a.
Daga cikin ayyukan kungiyar ta (LESPADA) sun hada da wayar da kan Al’umma a gurare daban-daban kamar makarantu, kasuwanni da duk wani wuri na taron jama’a harma da kulawa da wadanda matsalar shaye-shaye ta shafa daga bisani a taimaka rayuwar su ta fuskar Sana’o’i da aikin yi musamman matasa.
kazalika Ambassador Maryam Hassan ta kara da cewa daga cikin abubuwan da suke sa matasa na fadawa shaye-shaye akwai sakacin da iyaye su ke yi wajan kulawa da tarbiyyar ya’yansu, da kuma rashin sauke nauyin da Allah ya dora masu na tarbiyyar da dawainiyar gida.
Guda daga cikin masu rajin matasa sun zama matane na kwarai Comard Danmallan mai shayi bakin Abatúwa ya bayyana cewa dukkanin Al’umma sai sun taimaka wajan kulawa da tarbiyyar matasa, musamman bangaran shaye-shaye wanda yawanci shine yake tunzawa don aikata munanan ayyuka da lalata lafiya jiki dana Rohi.
Daga karshe Danmallan ya shawarci gwamnati da ta hada kai da irin wadannan kungiyoyi na inganta Rayuwa Al’umma da kuma ba su goyan bayan wajan yadda za a tsafatace jihar Kano daga Shaye-shaye wanda hakkan zai bukasa tattalin arziki da zaman lafiya a tsakanin jama’a.