‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana matakin da Sarkin Gaya ya dauka na janye sarautar Wazirin Gaya daga hannun tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, a matsayin abin takaici da rashin adalci.

‎A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Kano, ta bayyana cewa har zuwa wannan lokaci da take fitar da jawabin nata, Alhaji Usman Alhaji bai karɓi wata takardar hukuma da ke tabbatar da janye sarautar daga gare shi ba.

InShot 20250309 102512486
Talla

‎Kungiyar ta bayyana cewa, tun bayan soke masarautun gargajiya da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi a shekarar 2023, Usman Alhaji tare da wasu manyan masu rike da mukaman sarauta sama da guda 100, sun daina halartar fadar Sarkin Gaya.

‎A cewar kungiyar, daga baya Sarkin Gaya ya nemi a dawo da wasu daga cikin masu sarautar ciki har da Alhaji Usman Alhaji, sai dai gwamnatin Kano ta ki amincewa da sunansa cikin jerin wadanda za su dawo da mukamansu.

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

‎ “Ko da ace yana kan kujerar Wazirin Gaya ne, akwai tsari da ya kamata a bi kafin a janye masa mukami. Dole ne a fara da gargadi, a tuhume shi sannan a ba shi damar kare kansa. Amma abin mamaki, ba daya daga cikin wadannan matakai aka bi ba,” in ji sanarwar kungiyar.



‎Kungiyar ta ce abin da ya kara bata mamaki shi ne, daga cikin jerin wadanda gwamnati ta ki amincewa da su, sai Usman Alhaji kadai aka fito da sanarwar janye sarautarsa.

‎ “Duk da haka, ya yi aiki tukuru a matsayin Wazirin Gaya tsawon shekaru uku, lokacin da masarautar ke matsayin mai daraja ta farko. Har bayan rasuwarsa, mutane za su ci gaba da kiran shi da Wazirin Gaya saboda irin gudunmawar da ya bayar,” in ji kungiyar.

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

‎Martani Kan Zargin Tada Hankali

‎Kungiyar ta kuma yi karin haske kan zargin da wasu ke yi mata na kokarin tada hankalin jama’a, inda ta bayyana cewa wannan zargi ba shi da tushe balle makama.

‎Kungiyar ta bayyana cewa, taron manema labarai da suka gudanar a ranar 11 ga Yuni, 2025, domin bayyana matsayinsu kan cika shekaru biyu da gwamnatin NNPP ta yi a Kano, bai da alaka da neman tada fitina kamar yadda wasu kungiyoyi 20 suka shigar da kara a kansu.

‎A cewar kungiyar, daga bisani, daya daga cikin kungiyoyin da ake kira masu shigar da kara wato Dakata Community Development Association (DACKODA) ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta daga wannan kara.

‎Kungiyar ta ce takardar janye sunan DACKODA daga cikin masu shigar da kara ta iso gare su, wadda wani Michael Nworisa, wanda suka ce dan asalin Kano ne, ya rattaba hannu a kanta.

‎ “A bayyane yake wasu daga cikin kungiyoyin da ake kiransu a matsayin masu shigar da kara, ma ba su da masaniya game da wannan batun,” in ji sanarwar.



‎Sake Tsayawa Kan Matsayinsu

‎Kungiyar ta kuma bayyana cewa maimakon gwamnatin Kano ta duba wadannan matsaloli ta gyara kura-kuranta, sai ma ta ci gaba da amfani da kalaman batanci da cin mutunci kan Alhaji Usman Alhaji.

‎> “Mun san wadanda ke haddasa tarzoma da amfani da matasa masu shan miyagun kwayoyi da daukar makamai don tayar da hankali. Amma mu ba mu cikin wannan tsari. Muna tafiya ne bisa doka da oda,” in ji kungiyar.



‎Dangane da korafinsu kan karbar bashi daga kasashen waje da gwamnatin Kano ke ci gaba da yi, kungiyar ta ce bayan sake duba lamarin, sun fahimci cewa mafi yawan bashin yana daga cikin tsofaffin basussukan da aka gada daga gwamnatocin baya. Saboda haka, sun janye wannan korafi, sai dai sauran batutuwan da suka gabatar suna nan daram.

‎ “Za mu ci gaba da bayyana gaskiya bisa doka da oda, kuma ba za mu yarda a ci mutuncin Alhaji Usman Alhaji ko kuma a fake da siyasa a ci zarafin mutanen kirki ba,” a cewar kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...