Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Date:

Daga Abubakar Sayeed

Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar kano Com. Ibrahim Abdullahi Waiya ya bukaci Jami’an yada labarai na kananan hukumomin jihar da su cigaba da aiki da Kwarewa wajen wayar da kan al’umma musamman kan batun da ya shafi inganta harkokin kiwon lafiya .

” Babu shakka za mu cigaba da ba ku dukkanin gudunmawar da kuke bukata domin ganin Kuna cigaba da gudanar da aikin ku bisa Kwarewa da kuma tallafawa gwamnati da al’ummar jihar Kano”.

InShot 20250309 102512486
Talla

Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin da yake bude taron Bita na yini biyu ga Jami’an yada labarai na kananan hukumomi 44 kan muhimmancin Kula da cin Abinchi Mai Gina Jiki don Kula da lafiya.

” Yace ana sa ran bayan kammala bitar Jami’an yada labaran za su yi amfani da Ilimin da suka samu wajen wayar da kan al’ummar kananan hukumomin da suke aiki saboda su rika cin Abinchi Mai Gina Jiki, don magance matsalar mace-macen da ake samu a Kano saboda wasu cututtuka da suke da alaka da cimma”.

Waiya ya ce ya gamsu da rawar da Jami’an yada labaran suke takawa wajen ganin sun sauke nauyin da aka dora musu, wanda ya ce hakan ce ta sa tunda ya Zama Kwamishina ya ke shirya musu bitoci don kyautata aiyukansu .

“Ina kira a gare ku da ku rika amfani da damarku wajen Isar da sakonni ko wayar da kan al’umma yayin duk wani taron da ake yi karamar hukumar da ku ke aiki, hakan zai taimakawa wajen Kai sakonninku cikin al’umma cikin sauki” . Inji Waiya

Kwamared Waiya ya kuma ba da tabbacin nan ba da jimawa ba ma’aikatar sa za ta samar da kayan aiki na zamani ga Jami’an yada labarai na kananan hukumomin don inganta aikinsu.

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Ya kuma ce daga yanzu zai saka gasa a tsakanin Jami’an ta yarda duk wata za a rika fitar da wadanda suka fi yin kwazo a watan , inda ya yi alkawarin ba da kyauta ga wadanda suka yi nasara.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana gidiyarsu ga kwamishin bisa yadda ya shirya musu bitar , inda suka ce sun amfana Sosai da bitar kuma za su duk mai yiwuwa don aiwatar da abun da suka koya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...