Zawiyyar Malam Bala Maiyafe ta Shirya taron yiwa Kasar addu’ar Zaman Lafiya

Date:

Daga Saminu Ibrahim Magashi
Zawiyar malam Bala maiyafe dake unguwar adakawa a jihar kano ta hada gangamin taron yiwa kasa addu’oin neman zaman lafiya, yayin da a gefe guda Kuma zawiyar tayi hubbasa wajan ganin ta shiga sahun masu tallafawa marasa karfi da marayu ta hanyar Samar da Gidauniyar.
Yayin taron addu’ar an yi saukar  karatun Ishiriniya, tare da gabatar da makaloli daga bakin malamai da dama, da niyyar jawo hankalin al’umma da kuma kara sanin muhimmancin zaman lafiya da neman ilmin addini da kuma ruko da Zumunci.
Datake bayani Shugabar Gidauniyar Dr Atika Bala Maiyafe, ta bayyan cewa sunyi wannan yunkurine domin zaburar da masu hannu da shuni wajan shirya irin wanann tarurruka domin yiwa qasa addu’a.
Dr. Atika ta kuma kara da cewa lokaci zuwa lokaci za su rika shirya irin Wannan taron addu’ar domin nemawa kasar nan dauwamammen Zaman Lafiya.
Taron dai yasamu halittar dumbin al’umma da suka hada da malam Sheikh Ibrahim Khalil, Sheikh Umar Sani Fagge, da sarkin fawa na jihar kano da dai sauran muhiman mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...

Sarkin Yaƙin Garko, ya ɗauki nauyin dubawa da raba magunguna kyauta ga marasa lafiyar 1400 a Garko

  Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al'umma, kuma ɗan jam'iyyar...

NAHCON ta yi jigilar Maniyatan Nigeria Sama da 24,000 zuwa Saudiyya a kwanaki 10

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar Kula da aikin hajji ta...