Mataimakin shugaban majalisar dattawa ta ƙasa , Sanata Barau Jibrin, ya bai wa ɗalibai 1,000 cikakken tallafin karatu wanda darajarsa ta kai kimanin Naira 800,000 ga kowane ɗalibi.
Yayin ƙaddamar da shirin tallafin a Jami’ar Bayero da ke Kano a ranar Asabar, Barau ya ce manufar ita ce magance matsalolin kuɗin karatu da matasa ke fuskanta tare da ba su damar samun ingantacciyar ilimi.
Sanata Barau, wanda Sanata Kawu Sumaila ya wakilta a wajen raba takardar samun gurbin karatu, ya bayyana cewa daliban za su yi karatu ne a Jami’ar Taraiya ta Dutsinma da ke jihar Katsina.
A cewa Sumaila, ɗaliban da suka amfana sun fito ne daga Kano-ta-Kudu da Kano-ta-Tsakiya, inda ya ce za su yi karatun ne a cibiyoyin jami’ar biyu na Gaya da kuma birnin Kano.
An Yanka ta Tashi Game da Digirin Girmamawar da aka Baiwa Rarara
Ya ce ilimi shi ne babban abun da ya baiwa fifiko, inda ya ƙara da cewa wannan shiri na nuna jajircewar Barau wajen tabbatar da makomar Najeriya ta hanyar ilmantar da matasa da kuma ba su ƙarfi.
Ya shawarci waɗanda suka amfana da su yi amfani da damar yadda ya kamata, yana mai tunatar da su cewa wannan tallafi ba wai taimakon kuɗi kaɗai ba ne, illa kuwa kira ne zuwa ga hidima da kuma neman nagarta.
Sanata Kawu Sumaila ya kuma ɗauki nauyin sufuri na Naira 20,000 ga kowanne ɗalibi.
Karamin Ministan Harkokin Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Atah, ya yaba da shirin, yana mai cewa wannan misali ne na ayyukan jama’a da sauran shugabanni ya kamata su yi koyi da shi.

Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Haruna Musa, ya jinjina wa wannan tsari, yana mai cewa ya zo a kan gaba kuma zai sauya al’amura sosai.
Wasu daga cikin masu cin gajiyar shirin, Fathiyya Musa da Hauwa Abubakar Ibrahim, sun bayyana godiyarsu tare da alkawarin yin amfani da damar yadda ya kamata.