Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Date:

Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa ransa sakamakon harbin kansa da bindiga da yayi bisa kuskure lokacin da yake bakin aiki a jihar Kano.

A cewar daily trsut, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:40 na safiyar ranar Asabar a unguwar Hotoro.

Rahotanni sun ce jami’in da ke aiki a rundunar ƴansandan jihar Kano, ya shiga bandaki a harabar Kamfanin Basnaj Global Resources Limited, lokacin da bindigarsa ta harba.

Binciken farko ya nuna cewa Ibrahim ya harbe kansa a ciki yayin da yake tsugunawa da bindigarsa kirar AK-47 da ke rataye a wuyansa.

Bindigar mai lambar rajista GT 4177, an same ta tare da harsashi guda daya da ya harba, yayin da aka lissafa harsasai 29 daga cikin 30 da aka ba shi a farko.

An garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa, sannan aka kai gawarsa dakin ajiye gawa domin yi masa gwajin gano musabbabin mutuwarsa.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa har yanzu ana bincike kan lamarin, kuma za su bayyana sakamakon nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...