Kungiyar ODPMNigeria ta shirya taron tattaunawa da matasa a Bichi

Date:

Daga Ahmad Isa Getso

 

Ƙungiyar Rajin Kawo Sauyi da Cigaba da a siyasa tare da haɗin guiwar Majalisar Matasa ta Ƙasa (NYCN) reshen ƙaramar hukumar Bichi, ta gudanar da taron tattaunawa na musamman da matasa domin nazartar matsalolin tsaro a jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.

A yayin taron, mahalarta sun yi duba kan yadda matsalar tsaro ta tsananta, tare da nazarin rawar da matasa da kungiyoyinsu za su taka wajen kawo ƙarshen lamarin.

Ƙungiyar ODPMNigeria ta jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin matasa da hukumomin tsaro, tare da yin kira ga matasa su rinka bayar da shawarwari masu amfani da kuma taka muhimmiyar rawa wajen samar da mafita, maimakon shiga cikin masu haddasa matsalar.

Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Haka kuma, an yaba da irin gudummawar da reshen Majalisar Matasa ta Ƙasa (NYCN) na Bichi ya bayar, wanda ya taimaka wajen tabbatar da nasarar taron.

Mahalarta taron sun bayyana jin daɗinsu da kuma sha’awar ganin irin wannan tarurruka suna ci gaba da gudana a sauran sassan jihar Kano.

Taron ya ƙare da kira ga matasa da su kasance jakadu na zaman lafiya tare da yin aiki kafada da kafada domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Kano da Nijeriya gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...