Daga Rukayya Abdullahi Maida
Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta bukaci al’ummar Musulmin Nigeria da su fara duban jinjirin watan almuharram na shekara ta 1447.
“Gobe Laraba 25 ga watan yuni 2025, ita ce daidai da 29 ga watan zulhijja na shekara ta 1446 don haka ita ce ranar da za a fara duban jinjirin watan almuharram na sabuwar shekarar musulunci”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin musulunci na fadar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo wali Junaidu ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu
Sanarwar duk wanda ya ga watan ya sanar da wani basarake mafi kusa da shi domin mika sanarwar ga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi domin tantancewa.
Kadaura24 ta watan Almuharram dai shi ne wata na farko a kalandar addinin musulunci.